Kashim Ibrahimali123k Lvg.PedDKhseeix Ww ap ad.o Ptwiki
| Kashim Ibrahim | |
|---|---|
|
| |
| Rayuwa | |
| Haihuwa | 10 ga Yuni, 1910 |
| ƙasa | Nijeriya |
| Mutuwa | 25 ga Yuli, 1990 |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
| Kyautuka |
ẓer
|
Kashim Ibrahim (Shettima) (10 ga Yuni 1910 zuwa 25 ga Yuli 1990)[1] mutumin Kanuri ne kuma ɗan siyasa, ya riƙe shugabancin gargajiya a masarautar Borno kuma minista ne na ayyukan jama'a a shekarun 1950s. Yazama Waziri a Masarautar Borno bayan korar Wazirai biyu da akayi sakamakon zarginsu da akeyi akan yadda suke gudanar da ayyuka a masarautar. Yakasance na hannun daman Sardauna Ahmadu Bello.[2]
Rayuwarsa[gyara sashe | Gyara masomin]
An haife Ibrahim a garin mazabar Gargar, Yerwa daga gidan Ibrahim Lakanmi.[3] Yafara karatun sa da koyon larabci da Quran kafin yaje Borno Provincial School a shekara ta 1922. A kuma 1925, Yasamu shiga Kwalejin Horo ta Katsina inda ya kammala karatun sa da sakamakon malunta a 1929. Ya fara aiki a matsayin Malami a 1929 a Borno Middle School sannan daga shekara ta 1933, yazamanto Provincial Visiting Teacher. Inda daga bisani akai masa Karin girma yakaiga matsayin Senior Visiting Teacher and education officer for the province of Borno. An bashi sarautar Shettiman Borno a 1935 daga nan ne akasansa da Shettima Kashim. Ya shiga siyasa a 1951-52, sanda aka zabesa zuwa majilisar arewacin Najeriya (Northern Regional Assembly), he as nominated from the North as a cabinet nominee. Daga nanne aka zabeshi a matsayin ministan tarayya na Ayyukan Jama'a bayan nan kukuma yazama ministan Ilimi.
A shekarar 1956, Shehun Borno yanada shi Wazirin Borno.[4] Waziri Ibrahim yazama Gwamnan yankin Arewacin Najeriya a 1962, yacigaba da mulkinsa har saida akayi juyin mulkin soji a 16 ga watan Janairun shekara ta 1966 wanda takawo mulkin Manjo General Johnson Aguiyi-Ironsi.[5] An nadashi CBE a 1960 kuma wanda yanashi shine KCMG a 1962.[6]
Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]
- ↑ "Ibrahim, Sir Kashim", in Christopher Osadiaye Orumwese Ugowe, Eminent Nigerians of the twentieth century, Hugo Books, 2000, p. 155.
- ↑ Ahmadu Bello, My Life, Cambridge University Press, 1962, p. 31.
- ↑ cite web |url=http://www.sharia-in-africa.net/media/publications/sharia-implementation-in-northern-nigeria/vol_1_5_chapter_1_part_II.pdf |title=The Settlement of 1960: Who was Who |work=Sati Fwatshak and Philip Ostien |accessdate=2015-08-28
- ↑ Rosalynde Ainslie, Catherine Hoskyns, Ronald Segal. Political Africa: A Who's Who of Personalities and Parties, New York: Frederick A. Praeger, 1961, p. 128.
- ↑ "Provinces and Regions of Nigeria". WorldStatesmen. Retrieved 2010-05-28.
- ↑ Oxford Dictionary of National Biography